Independent African news, markets, culture and politics.
1 min read

Majalisa ta yi sammacin kwamishanan Nasarawa

Majalisar dokokin jihar Nasarawa tayi sammacin kwamishinan muhalli da albarkatun kasa, Yakubu Kwanta, domin ya bayyana a gaban majalisar a […]

Media Talk Africa default story image

Majalisar dokokin jihar Nasarawa tayi sammacin kwamishinan muhalli da albarkatun kasa, Yakubu Kwanta, domin ya bayyana a gaban majalisar a ranar Litinin, 16 ga Disamba, 2024, bisa tuhumar rashin biyayya.

Majalisar dai ta sha alwashin daukar tsatstsauran mataki kansa muddin ya gaza bayyana a gabanta.

Shugaban Majalisar, Danladi Jatau, ya bayar da wannan umarnin lokacin da shugaban kwamitin Majalisar kan Gidaje da Muhalli, wanda kuma ke wakiltar mazabar Keana, Muhammad Adamu Omadefu, ya gabatar da batun yayin zaman Majalisar a Lafiya, babban birnin jihar a jiya Alhamis.

Kwamishinan zai bayyana ne domin kare kasafin kudin ma’ikatar sa, a kasafin kudin 2025 da gwamnan ya gabatar.

Shugaba majalisar ya bayyana cewa ba za su lamunci kowanne irin rashin biyayya daga kowanne kwamishina a jihar ba.

Ifunanya

Unearthing the truth, one story at a time! Catch my reports on everything from politics to pop culture for Media Talk Africa. #StayInformed #MediaTalkAfrica

Comments are closed for this story.

Scroll to Top